Tarayyar Turai (EU) ta bayyana cikakken goyon bayanta ga mutanen Najeriya da suka gamu da tashin hankali a wasu yankuna na ƙasar, musamman a yankin kudu da arewa maso gabas, inda aka kai hare-hare a baya-bayan nan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun harkokin ƙetare da tsaron Tarayyar Turai, Anouar El Anouni, ya fitar ranar Talata, kuma ta isa ga Vanguard, kungiyar ta ce ta lura da kalaman da gwamnatin Amurka ta yi kan Najeriya.
Da yake amsa tambaya kan ko Tarayyar Turai za ta mayar da martani kan barazanar da Amurka ta yi wa Najeriya, El Anouni ya ce, “Tarayyar Turai ta lura da furucin gwamnatin Amurka game da Najeriya. Muna bayyana cikakken goyon bayarmu ga dukkan al’ummomi da iyalai da suka shiga cikin tashin hankali, musamman waɗanda suka sha wahala sakamakon hare-haren da suka faru kwanan nan a yankin kudu da arewa maso gabas na Najeriya.”
Mai magana da yawun ya kara da cewa Tarayyar Turai za ta ci gaba da kare haƙƙin ɗan adam da ’yancin addini, tare da kare ƙananan ƙabilu da sauran al’umma.
“Tarayyar Turai za ta ci gaba da jajircewa wajen kare ’yancin yin addini da yarda, da kuma tabbatar da tsaron dukkan al’umma musamman ƙananan ƙungiyoyi. Muna jaddada bukatar zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin yanki, kabila, siyasa ko addini ba,” in ji El Anouni.
Ya kuma bayyana cewa akwai dalilai da dama da ke haddasa tashin hankali a Najeriya, inda addini kawai yake daga cikin su a wasu lokuta.
“Mun fahimci cewa akwai abubuwa masu yawa da ke haddasa rikice-rikice a Najeriya, kuma addini ba shi ne babban dalili ba sai a wasu yanayi,” ya ƙara da cewa.
El Anouni ya ce Tarayyar Turai tana ci gaba da aiki tare da hukumomin Najeriya domin kawo karshen matsalolin tsaro.
“Tarayyar Turai na aiki tare da hukumomin Najeriya wajen aiwatar da shirye-shirye da dama don hana tashin hankali, ƙarfafa zaman lafiya, da taimakawa waɗanda rikici ko tilastaccen ƙaura ta shafa,” in ji shi.





