Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC) ta samu wani babban nasara a ci gaban yunkurinta na dakile haramtattun ayyukan hakar ma’adinai da kuma kare albarkatun kasa na ƙasa. Rundunar musamman ta NSCDC mai kula da hakar ma’adinai a yankin Kudu maso Kudu ta samu nasarar rufe wasu wuraren tono da hakar yashi marasa izini a Jihar Rivers.
Wannan aiki ya nuna jajircewar hukumar wajen kare muhimman kadarorin ƙasa da tabbatar da bin dokokin da ke tsara hakar ma’adinai a Najeriya abin da ya yi daidai da hangen nesa na Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi.
Jagoran wannan samame, DSC Emmanuel Abiahu, wanda shi ne kwamandan rundunar hakar ma’adinai ta Kudu maso Kudu, ya tabbatar da cewa an rufe wurare da dama da ake gudanar da haramtattun ayyukan hakar ma’adinai, hakar duwatsu da zubar da yashi a Ƙaramar Hukumar Eleme ta Jihar Rivers.
“Matsayarmu a bayyane take tabbatar da cikakken bin dokokin hakar ma’adinai a dukkan sassa,” in ji DSC Abiahu. “Muna gano wuraren da ake aikin ba bisa ka’ida ba ta hanyar sahihin bayanan leƙen asiri, muna kuma rusa su tare da gurfanar da masu laifi. Wannan gargadi ne na ƙarshe ga duk masu wannan aiki a yankin Kudu maso Kudu: ku gyara lasisoshinku nan da nan, in ba haka ba za ku fuskanci cikakken hukunci.”
NSCDC ta sake jaddada kudirinta na kare kadarorin tattalin arziƙin ƙasa da kuma tabbatar da dorewar muhalli. Hukumar ta ce za ta ci gaba da yin aiki tare da hukumomin gwamnati na cikin gida, shugabannin al’umma, da sauran hukumomin da abin ya shafa domin kawar da haramtattun ayyukan hakar ma’adinai.
Haka kuma, hukumar ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su kasance masu lura da faɗakarwa, su rika ba da rahoto idan suka ga wani aikin tono ko hakar yashi da ake gudanarwa ba bisa ka’ida ba a cikin al’ummominsu — domin wannan aiki na kare albarkatun ƙasa abu ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa.




