Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba da tallafin motoci uku na Toyota Hilux ga Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Jigawa, domin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta karfin aikin jami’an tsaro a fadin jihar.

An mika motocin ne a ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) da ke Dutse, ta hannun Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Musamman da Kula da Majalisar Gwamnati, Bello Datti, tare da Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Tsaro, Dakta Usman Muhammad Jahun. Wannan gudummawa na daga cikin shirin gwamnati na ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kare muhimman kadarorin kasa.
Da yake karɓar motocin, Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, Kwamanda Muhammad Kabir Ingawa, ya mika godiyarsa ta musamman ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi (FCA), bisa wannan kyauta mai muhimmanci da kuma goyon bayansa na dindindin ga hukumomin tsaro a jihar.
Kwamanda Ingawa ya bayyana wannan mataki a matsayin “shaida ta gaskiya kan jajircewar Gwamna wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro wajen magance matsalolin tsaro.” Ya tabbatar da cewa motocin za a yi amfani da su wajen gudanar da sintiri, amsa gaggawa, da kuma kare muhimman gine-gine da kadarorin gwamnati musamman a yankunan karkara da iyakoki.
Haka kuma, Kwamandan ya sake nanata kudirin hukumar na ci gaba da bin ka’idojin aiki, kwarewa, da ladabi wajen gudanar da ayyukanta na doka, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro mai dorewa a fadin Jihar Jigawa.
Wannan tallafi na gwamnati zai taimaka matuƙa wajen ƙara ƙarfin motsi, gaggawar amsa kiran gaggawa, da kuma fitowa fili wajen gudanar da ayyukan tsaro a cikin kananan hukumomi 27 na jihar, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.




