Babban Hafsan Rundunar Sojan Ruwa na Najeriya (CNS), Vice Admiral Idi Abbas, ya amince da sauya matsayi da sake tura manyan jami’ai 65 masu mukamin Rear Admiral zuwa muhimman wuraren aiki daban-daban a cikin rundunar, hedikwatoci, da cibiyoyin horo na haɗin gwiwa da sauran bangarori na tsaro.
A cewar sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Commodore Adams Aliu, ya fitar ranar Litinin, wannan sauyin wurin aiki na cikin shirin sabunta tsarin rundunar domin ƙara haɓaka aiki, ƙwarewa, da inganta tsarin jagoranci a cikin rundunar.
A sabon tsarin da aka fitar, an nada wasu daga cikin manyan jami’ai a muhimman mukamai na jagoranci da dabaru a cikin rundunar da kuma cibiyoyin tsaro na ƙasa.
Wasu daga cikin sabbin nade-naden sun haɗa da:
- Rear Admiral Suleiman Abdullahi – Babban Daraktan Sashen Kayayyakin Aiki, Hedikwatar Rundunar Sojan Ruwa, Abuja
- Rear Admiral Kasim Bushi – Darakta Janar, Cibiyar Koyon Harkokin Ruwa ta Najeriya (IMION)
- Rear Admiral Suleiman Dahun – Daraktan Hulɗar Tsaro, Hedikwatar Tsaro (DHQ)
- Rear Admiral Abdullahi Ahmed – Kwamandan, Makarantar Tsaro ta Ƙasa (National Defence College)
- Rear Admiral Musa Katagum – Babban Daraktan Ayyuka, Hedikwatar Rundunar Sojan Ruwa
- Rear Admiral Fredrick Damtong – Babban Daraktan Injiniyanci, Hedikwatar Rundunar Sojan Ruwa
- Rear Admiral Abdul-Rasheed Haruna – Babban Daraktan Horo, Hedikwatar Rundunar Sojan Ruwa
- Rear Admiral Hamza Ibrahim – Manajan Darakta Janar, Kamfanin Navy Holdings Limited
- Rear Admiral Abubakar Mustapha – Kwamandan Rundunar Sojan Ruwa ta Yamma (Western Naval Command)
- Rear Admiral Chidozie Okehie – Kwamandan Rundunar Sojan Ruwa ta Gabas (Eastern Naval Command)
- Rear Admiral Suleiman Ibrahim – Kwamandan Rundunar Sojan Ruwa ta Tsakiya (Central Naval Command)
- Rear Admiral Ebiobowei Zipele – Kwamandan Rundunar Horo ta Sojan Ruwa (NAVTRAC)
Sauran jami’an kuma an tura su zuwa sassa daban-daban kamar na gudanarwa, dabaru, ayyuka, manufofi, da injiniyanci — a cikin hedikwatar rundunar da kuma Hedikwatar Tsaro.
Vice Admiral Abbas ya bayyana cewa wannan sauyin wurin aiki na da nufin kawo sabuwar kuzari cikin jagorancin rundunar, ƙarfafa haɗin kai tsakanin rundunoni, da ci gaba da tabbatar da nasarorin da rundunar ta samu a yaƙin da take yi da laifukan ruwa.
Rundunar Sojan Ruwa ta bayyana wannan sauyi a matsayin sabon tsari na ƙarfafa aiki, inganta horo, da tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa a dukkanin matakan jagoranci.




