Yayin da shirye-shiryen zaben gwamnan Jihar Anambra na ranar 8 ga Nuwamba ke kara zafi, mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya yi gargaɗi ga ‘yan siyasa da magoya bayansu da su guji tashin hankali, yana mai cewa duk wanda ya tayar da rikici a lokacin zaben zai fuskanci martani mai tsauri da babu sassauci.
Ribadu ya yi wannan gargadi ne a Abuja, ta bakin Darakta na Sashen Tsaron Cikin Gida na Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro (ONSA), Hassan Yahaya Abdullahi, inda ya tabbatar da cewa dukkan matakan tsaro sun kasance a shirye domin tabbatar da zabe mai zaman lafiya da inganci.
“Dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu dole su wayar da kai ga zaman lafiya, su kuma fadakar da magoya bayansu da su yi biyayya da doka. Duk wani yunkuri na tada hankali za a fuskance shi da cikakken karfi da tsauri,” in ji Ribadu.
NSA din ya kara jaddada cewa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya tare da sauran hukumomin tsaro sun shirya sosai don kare lafiyar jama’a kafin, yayin, da bayan zaben.
“Rundunar ‘Yan Sanda ce babbar hukuma mai alhakin tsaron zabe, tare da hadin kai daga sauran hukumomin tsaro, za mu tabbatar da tsari da zaman lafiya a duk fadin Jihar Anambra. Muna kira ga ‘yan kasa da su hada kai domin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali wanda zai nuna dabi’un dimokuradiyyarmu,” in ji Ribadu.
A wani bangare kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya bayyana cewa hukumar ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben daga bangaren kayan aiki da na aiki.
Ya ce zaben zai gudana ne a rumfunan zabe 5,718 daga cikin 5,720 na jihar, yayin da rumfunan biyu ba za a yi zabe ba saboda babu masu kada kuri’a da aka yi wa rajista a wuraren. Ya kara da cewa ma’aikatan INEC kusan 24,000 ne za a tura don gudanar da zaben.
Farfesa Amupitan ya kuma bayyana dalilin tsawaita wa’adin karbar katin zabe (PVC) har zuwa Lahadi, 2 ga Nuwamba, bayan da rahotanni suka nuna cewa kashi 63.9 cikin 100 na masu zabe ne kawai suka karbi katunsu.
“Wannan karin lokaci zai bai wa masu zabe damar karbar katinsu a cibiyoyin da aka tanada a fadin kananan hukumomi 326. Burinmu shi ne kada wani dan kasa da ya cancanta ya rasa damar kada kuri’a,” in ji shi.
Shugaban INEC ya jaddada cewa dole ne kowane mai zabe ya karbi katinsa da kansa, babu wanda zai iya karbar na wani. Ya kuma yaba wa mutanen Anambra bisa hakuri da hadin kai, yana rokon su da su ci gaba da shirye-shiryen su domin gudanar da zabe cikin lumana.
Farfesa Amupitan ya kara da cewa hukumomin tsaro sun gano wasu wurare masu hadarin tashin hankali a jihar, inda ya bukace su da su ci gaba da hadin kai wajen kare ma’aikatan zabe, kayan aiki da masu kada kuri’a.
Ya kuma sake jan hankalin ‘yan siyasa kan cinikin kuri’a, yana cewa hukumar ba za ta lamunci sayen kuri’u ba.
“Duk wani yunkuri na sayen kuri’a kafin ko yayin zabe za a hana shi. Muna aiki tare da hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci domin dakile wannan mummunar dabi’a,” in ji shi.
A halin da ake ciki, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya amince da tura jami’an ‘yan sanda 45,000 domin tsaron zaben.
IGP ɗin, wanda Kwamishinan ‘Yan Sanda na Rukuni na Musamman (Special Intervention Squad), Abayomi Shogunle, ya wakilta, ya bayyana cewa za a fara tura jami’ai daga ranar 1 ga Nuwamba domin gudanar da ayyukan tsaftacewa da kama masu yuwuwar tayar da zaune tsaye kafin zaben.
Ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar da tsaro domin bai wa ‘yan kasa damar yin zabe cikin kwanciyar hankali da tsoron Allah.
“Mun kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya da hana duk wani yunkuri na tayar da hankali kafin, yayin, da bayan zabe,” in ji IGP ɗin.





