Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC) ta sake tabbatar da kudurinta na ci gaba da kare Muhimman Kadarorin Kasa da Muhimman Gine-gine (CNAI) domin tabbatar da tsaron kasa da ci gaban tattalin arziki. Wannan jigo ne ya dauki muhimmiyar rawa a Taron Tsaro na Kasa da Kyaututtuka na shekara ta 2025 wanda Ƙungiyar ‘Yan Jaridar Tsaro ta Intanet (NAOSNP) ta shirya, a dakin taro na Lagos Oriental Hotel, Victoria Island, ranar Talata, 21 ga Oktoba, 2025.
Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, PhD, mni, OFR, ya samu wakilcin Kwamandan Jihar Legas, Mista Keshinro Adedotun, a wannan taron.
Yayin tattaunawar kwamitin da taken “Kare da Tsare Albarkatun Tattalin Arzikin Najeriya: Kira Ga Hidima,” Mista Adedotun ya yabawa NAOSNP bisa jajircewarta wajen samar da dandalin tattaunawa kan batutuwan tsaro da kuma hadin gwiwar hukumomi don inganta tsarin tsaro a kasar. Ya kuma bayyana irin kokarin da hukumar ke yi wajen dakile barazanar tsaro, hana barna, da kuma tabbatar da kariyar muhimman gine-gine da kadarorin da suka da matukar muhimmanci ga cigaban kasa.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su tallafa wa hukumar NSCDC a yunkurinta na hadin gwiwa da gaskiya wajen yakar barna da satar kadarorin kasa da albarkatun tattalin arziki. Ya jaddada cewa gwamnati tana kara kokari wajen yakar cin hanci da rashawa da kuma fadada hanyoyin samun kudin shiga ta hanyoyi daban-daban.
A karshe, a cikin girmamawa ga jagoranci mai kyau da salon aiki na “Hadakar Jama’a” wajen kare kadarorin kasa, warware rikice-rikice, da tsare albarkatun tattalin arzikin kasa, Farfesa Ahmed Abubakar Audi ya samu lambar yabo ta NAOSNP 2025 Award of Excellence.




