Kwamandan Jihar Kano na Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), Kwamanda Bala Bawa Bodinga, ya sake jaddada kudirin shugabancinsa na tabbatar da ladabi, kwarewa da bin ka’idojin aiki a tsakanin jami’an hukumar.
Kwamanda Bodinga ya bayyana haka ne yayin duba Quarter Guard da kuma jawabi ga jami’ai da ma’aikata a wajen taron muster parade da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Kano, a ranar Talata.
A cikin jawabinsa, ya tunatar da jami’an cewa ladabi, jajircewa da bin ka’idojin aiki su ne ginshiƙan gudanar da aiki cikin inganci. Ya jaddada cewa kowane jami’i dole ne ya nuna aminci, gaskiya da kwarewa wajen aiwatar da aikinsa, domin wadannan dabi’u su ne ginshikin samun amincewar jama’a da ingantacciyar aiki.
Kwamandan ya kuma gargadi jami’an cewa shugabancinsa ba zai lamunci halayen rashin ladabi, sakaci ko kin bin doka ba, domin irin wadannan halaye suna lalata nagartar hukumar kuma suna kawo tarnaki ga cimma manufofin kare rayuka da dukiyoyin gwamnati.
Kwamanda Bodinga ya bukaci jami’an da su ci gaba da kasancewa masu jajircewa, gaskiya da daukar nauyin ayyukansu cikin amana. Ya karfafa musu gwiwa da su kare martabar hukumar ta hanyar nuna halin kirki, aiki tare da juna da kuma girmama tsarin umarni.
A karshe, ya tabbatar wa jami’an da cewa zai ci gaba da tallafa musu tare da kula da walwalar su da ci gaban sana’a, yana mai jaddada cewa a karkashin shugabancinsa, NSCDC ta Kano za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa ginshikin ladabi, bin ka’ida da nagartaccen aiki.



