Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a harin da ƴan bindiga suka kai a kauyen Layin Danauta, karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, ya karu zuwa mutum 13, bayan wasu uku daga cikin wadanda suka jikkata sosai sun mutu yayin da ake ba su kulawar lafiya.
Wannan sabon adadi ya karu daga farkon rahoton mutum tara, sannan goma, da aka tabbatar sun mutu a mummunan harin da ƴan bindigar suka kai kan mazauna yankin ba tare da jin kai ba.
Daga cikin wadanda suka mutu akwai matar ɗan sanda, wacce ƴan bindigar suka harba a gidansu da ke Kuyello yayin harin, inda daga bisani ta mutu a asibiti a Zariya.
A halin yanzu, iyalan wadanda abin ya shafa sun bayyana fushinsu kan yadda wasu kafafen yada labarai ke ƙoƙarin karkatar da gaskiyar lamarin, suna kiran harin “rikici tsakanin ƴan bindiga da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba,” maimakon bayyana shi a matsayin kai tsaye kisan gilla ga fararen hula.
Wani mazaunin yankin da ya yi magana a madadin iyalan da abin ya shafa, ya musanta rahotannin da ke yawo, yana mai cewa harin ya auku ne a cikin al’ummarsu ta Kuyello, ba a wani wurin hakar ma’adinai ba.
Ya ce, “Ƴan bindigar sun kashe dangi da abokanmu, sun jikkata da dama, sun yi garkuwa da wasu, sun fasa shaguna, kuma sun sace babura. Shin ƙananan yaranmu ma hakar ma’adinai suke? Ko kuwa aka kashe su a ma’adinai? Duk mutanen da aka kashe suna cikin Kuyello. Ko matar ɗan sandan da aka harba ta mutu jiya — ita ma mai hakar ma’adinai ce?
“Mun sani ana ƙoƙarin boye gaskiya don kare yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati ta yi da ƴan bindiga. Duk wanda ke yada ƙarya yana raina mutuwar mutanenmu marasa laifi. Mu dai muna so mu yi makoki cikin nutsuwa ba tare da ganin ana siyasantar da mutuwar ƙaunatattunmu ba.”
Mazauna yankin sun kuma nuna hotunan wasu daga cikin wadanda aka kashe, ciki har da ƙananan yara da matasa.
Rahotanni sun nuna cewa akwai tashin hankali a wasu kauyuka makwabtaka kamar Mamman Yarwa, Unguwan Gobirawa da Unguwan Gangare, saboda tsoron cewa ƴan bindigar za su iya dawowa.
Rahotanni na farko sun bayyana cewa yara mata uku ‘ya’yan Alhaji Salisu Maiwada suna cikin mutanen tara da aka fara tabbatar sun mutu. Sauran da aka kashe sun haɗa da maza aure biyar da saurayi guda ɗaya.
Wani majiyar ya bayyana harin a matsayin “tsararren farmaki,” inda ƴan bindigar suka kewaye kauyen Layin Danauta da ke cikin unguwar Kuyello da yamma, suka toshe hanyoyin shiga da fita, sannan suka fara harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba.
Wannan lamari ya sake jawo hankalin jama’a game da yadda matsalar tsaro ke ta ƙamari a Birnin Gwari, inda hare-haren ƴan bindiga ke ci gaba da hallaka mutane marasa laifi da raba al’umma da gidajensu.





