Sojojin Rundunar 2 Division/Sector 3 na rundunar sojin Najeriya, karkashin Operation FANSAN YAMA, sun samu nasarar kubutar da mutane 21 da aka yi garkuwa da su a wani samame da aka gudanar a jihohin Kwara da Kogi, ranar 17 ga Oktoba, 2025.
Ayyukan hadin gwiwa da sojojin 12 Brigade Lokoja da 22 Armoured Brigade Ilorin suka gudanar, ya haifar da ceto mutane 14 maza, mata 5, jariri daya, da kuma ’yan kasar China 4. Rahotanni sun bayyana cewa wadanda aka ceto sun fito ne daga wurare daban-daban a cikin jihohin biyu. Sakamakon matsin lamba da sojoji suka kara kan ’yan bindigar, sai suka tilasta musu sakin wadanda suke tsare da su, wasu daga cikinsu sun shafe fiye da watanni hudu a hannunsu.
Babban Kwamandan Runduna ta 2 (GOC) kuma kwamandan Sector 3 Operation FANSAN YAMA, Manjo Janar C.R. Nnebeife, wanda ke jagorantar ayyukan, ya tabbatar da cewa an bai wa wadanda aka ceto kulawar gaggawa da kayan tallafi domin su murmure daga wahalhalun da suka sha a hannun ’yan bindigar. Ya jajanta musu tare da tabbatar da cewa rundunarsa za ta ci gaba da kai farmaki kan dukkanin ’yan ta’adda da masu aikata laifuka a yankin.





