Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) na Jihar Gombe, Mataimakin Kwamandan Hukumar Kashe Gobara (DCF) S. M. Suleiman, ya hade da sauran shugabannin hukumomin tsaro da na kare lafiya wajen tarbar Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, a yayin ziyarar aikinta ta kwanaki biyu a Jihar Gombe.
A cikin wannan ziyara, Uwargidan Shugaban Kasa ta bude taron farko na “Gombe State Health Summit” da aka gudanar a Cibiyar Taron Kasa ta Gombe (International Conference Centre). Haka kuma ta kaddamar da wasu muhimman ayyuka da aka kammala a fadin jihar domin inganta ci gaba, jin dadin jama’a, da walwalar al’umma.
Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya sun kasance cikin shiri a Filin Jirgin Sama na Gombe da kuma Cibiyar Taron Kasa domin tabbatar da tsaro da kariya daga gobara a dukkan wuraren taron.
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, karkashin jagorancin Babban Kwamanda, CGF Olumide O. Samuel, tana sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, tabbatar da lafiya, da kuma ci gaban al’umma mai dorewa bisa tsarin manufofin Gwamnatin Tarayya.





