A cikin nuna hadin kai da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga gobara, kungiyar shugabannin hukumomin kashe gobara na jihohi da daraktoci (Association of State Fire Chiefs and Directors), wacce ta kunshi shugabanni daga jihohi 36 da hukumar kashe gobara ta Babban Birnin Tarayya (FCT), ta kai ziyarar ban girma ga Babban Kwamandan Hukumar Kashe Gobara ta Kasa (Federal Fire Service), Olumode Adeyemi Samuel, a babban ofishin hukumar da ke Abuja a yau.
Tawagar karkashin jagorancin Adeseye Abimbola Margaret, Babban Kwamandan Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas, ta taya CGF Olumode murna bisa nadin sa tare da tattaunawa kan hanyoyin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi, bunkasa kwarewar ma’aikata, da kuma daidaita ka’idojin tsaron gobara a fadin kasa.
A cikin jawabinsa, Babban Kwamandan ya nuna godiya bisa wannan ziyara tare da sake tabbatar da kudirin hukumar na ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga hukumomin kashe gobara na jihohi, yana mai jaddada muhimmancin aiki tare wajen inganta dabarun yakar gobara a fadin kasa.




