An gudanar da bikin kaddamar da daliban digirin bayan firamare (Postgraduate) na shekarar karatu ta 2025/2026 a Jami’ar Tsaro ta Najeriya (NDA) tare da hadin gwiwar Hukumar Kasa ta Kariya Daga Gobara (Federal Fire Service – FFS) a yau. Wannan ya nuna ci gaba wajen inganta ilimi da karfafa gwiwa a fannin kula da hadurra da gaggawa a Najeriya.
Wakilin Kwamandan Janar na Hukumar Kariya Daga Gobara, Kwamandan Jami’ar Koyon Harkokin Wuta ta Kasa, ACF Peter Umetali, ne ya gabatar da jawabi a madadin Kwamandan Janar, Dr. Olumode Samuel Adeyemi, FCNA, ACTI. Ya taya sabbin daliban murnar samun shiga shirin, yana kuma jan hankalinsu da su kasance masu ladabi, jajircewa, da bin ka’idodin makarantar.
ACF Umetali ya bayyana cewa wannan shiri dama ce ta musamman ga ci gaban sana’a da ilimi, musamman ganin yadda nau’o’in hadurra ke ta canzawa a duniya. Ya bukaci sabbin daliban da su amfana da damar da shirin ke bayarwa domin su zama masu bada gudunmawa wajen tabbatar da tsaro da dorewar kasa.
A nasa jawabin, Daraktan Sashen Hulda da Hadin Gwiwa na NDA, Farfesa B.J. Ajibuwa, ya gabatar da tsarin karatu, dokoki da hanyoyin gudanar da shirin. Ya jaddada muhimmancin bin ka’idodin jarabawa, da kiyaye mutuncin bincike da gaskiya a harkokin karatu. Farfesa Ajibuwa ya kuma bayyana cewa ana kammala sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa (MoU) tsakanin NDA da FFS domin kara dorewar shirin, fadada damar shiga, da kuma shirin samar da karin digirin bayan na farko (Advanced Postgraduate Degrees).
A nata jawabin, Dekanar Makarantar Digirin Bayan Firamare, Farfesa N.A. David, wacce ta wakilci Shugaban Harkokin Ilimi na NDA, ta taya daliban murna, tana yaba wa jajircewar jami’ar wajen tabbatar da kammala karatu cikin lokaci. Ta jaddada cewa jami’ar na da ingantaccen tsarin da ke mutunta halayya da kwarewa, tana kuma gargadin daliban da su guji satar aiki (plagiarism) da duk wani rashin gaskiya. Ta bukace su nemi ilimi da zai taimaka musu wajen samar da mafita ga matsalolin da ke fuskantar al’umma.
Shugaban shirye-shiryen karatun, Farfesa Oluwole, ya bukaci daliban da su guji karya dokoki, su kasance masu ladabi, da mutunta lokaci. Ya shawarce su da su nemi taimako idan sun fuskanci kalubale a fannoni na karatu ko na rayuwa, tare da inganta dabi’u masu kyau na gaskiya da daukar nauyi.
Hadin gwiwar dake tsakanin Jami’ar Tsaro ta Najeriya da Hukumar Kariya Daga Gobara, wacce aka kafa tun shekarar 2018, ta ci gaba da haifar da kwararru ta hanyar shirye-shiryen digirin PGD da MSc a fannin Gudanar da Hadurra da Rage Illolinsu (Disaster Risk Management). Wannan hadin gwiwa na nuna kudurin bangarorin biyu na kara karfin kasa wajen shawo kan hadurra ta hanyar ilimi, bincike, da koyon fasahohi na zahiri.
An kammala bikin kaddamarwar ne da rantsuwar shiga cikin al’ummar daliban digirin bayan firamare na Jami’ar Tsaro ta Najeriya.




