NSCDC Ta Kama Mai Safarar Wiwi a Kano, Ta Mika Wa Hukumar NDLEA Don Bincike

Hedikwatar Jihar Kano ta Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Ababen Gwamnati (NSCDC) ta kama wani mutum da ake zargin mai safarar tabar wiwi ne, sannan ta mika shi ga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakin doka.

Kwamandan Jihar Kano na NSCDC, Kwamanda Bala Bawa Bodinga, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Kano. Ya ce wannan kama na daga cikin kokarin hukumar wajen kawar da miyagu da masu safarar miyagun kwayoyi daga cikin al’umma.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a ranar Talata, 7 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 2:30 na safe, lokacin da jami’an NSCDC na sashen Doguwa suka samu sahihin bayanan sirri, suka tare babur da yake dauke da mutane uku da ake zargin suna safarar miyagun kwayoyi.

An gano wadanda ake zargin da sunaye Yusuf Alasan, mai shekaru 25, mazaunin garin Doguwa, tare da wasu mutum biyu, Muktar Musa da Musa Sani. Rahotanni sun nuna suna dauke da jakunkuna uku masu girman buhun sukari, cike da tabar wiwi, da ake kira Indian hemp ko Wiwi, suna jigilar ta daga Doguwa zuwa Kafau a karamar hukumar Doguwa ta Jihar Kano. An cafke su ne a kofar Riruwai cikin wannan karamar hukuma.

Kwamanda Bodinga ya ce an kammala binciken farko da hukumar ta gudanar, kuma bisa tsarin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro, an mika wadanda ake zargin tare da kayan da aka kama ga Hukumar NDLEA ta Jihar Kano domin ci gaba da bincike da kuma aiwatar da matakan doka da suka dace.

Ya kuma jaddada cewa NSCDC a karkashin jagorancinsa za ta ci gaba da kare dukkan muhimman kadarorin kasa da kuma karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen yakar miyagun ayyuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Kano.

Kwamanda Bodinga ya gode wa kafafen yada labarai bisa goyon bayan da suke bayarwa a kai a kai, tare da kiran su da su ci gaba da hadin kai domin wayar da kan jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.

  • Keji Mustapha

    Related Posts

    DEFENCE MINISTER MUSA FORMALLY ASSUMES DUTY IN ABUJA

    Nigeria’s Minister of Defence, General Christopher Gwabin Musa (Rtd), formally assumed duty today, 5 December 2025, at the Ministry of Defence headquarters, Ship House, Abuja. His arrival marked the beginning…

    KOMANDAN MINING MARSHALS YA KIRA GA ƘARIN HAƘƘOƘIN HADA-KAI TSAKANIN HUKUMOMIN TSARO

    Komandan Mining Marshals, John Onoja Attah, ya yi kira ga hukumomin tsaro na Najeriya da su ƙara zurfafa haɗin gwiwa, yana mai lura da cewa kalubalen tsaro da ke sauyawa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    DEFENCE MINISTER MUSA FORMALLY ASSUMES DUTY IN ABUJA

    DEFENCE MINISTER MUSA FORMALLY ASSUMES DUTY IN ABUJA

    KOMANDAN MINING MARSHALS YA KIRA GA ƘARIN HAƘƘOƘIN HADA-KAI TSAKANIN HUKUMOMIN TSARO

    KOMANDAN MINING MARSHALS YA KIRA GA ƘARIN HAƘƘOƘIN HADA-KAI TSAKANIN HUKUMOMIN TSARO

    MINING MARSHALS COMMANDER URGES DEEPER SECURITY AGENCY PARTNERSHIP

    MINING MARSHALS COMMANDER URGES DEEPER SECURITY AGENCY PARTNERSHIP

    FFS Kano Command Strengthens Workplace Safety Culture at NDIC Kano

    FFS Kano Command Strengthens Workplace Safety Culture at NDIC Kano

    Commandant Chinedu Revamps Female Squad, Flags Off School Protection Patrols

    Commandant Chinedu Revamps Female Squad, Flags Off School Protection Patrols

    psm