Hoto: ACC Attah
Kwamandan Rundunar Tsaro da Kare Muhalli ta Kasa (NSCDC) na Sashen Musamman Kan Hakar Ma’adinai, Assistant Commandant of Corps (ACC) Onoja John Attah, ya yi kira da a kara hadin kai da kuma samun cikakken goyon bayan doka a yaki da harkar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a fadin kasar nan. ACC Attah ya yi wannan kira ne yayin kaddamar da Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba, inda ya wakilci Commandant General na rundunar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi.
Ya jaddada cewa samun daidaituwar aiki tsakanin bangaren majalisar dokoki, hukumomin tsaro, al’ummomin yankuna, da sauran masu ruwa da tsaki na da matukar muhimmanci domin Najeriya ta iya shawo kan matsalar hakar ma’adinai ba bisa doka ba, tare da kare albarkatun kasa masu daraja da Allah Ya hore mata.
Yayin da yake jawabi a wurin taron, ACC Attah ya bayyana cewa matsalar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba na daya daga cikin manyan kalubalen tsaro da tattalin arziki da ke fuskantar Najeriya, inda kasar ke asarar sama da dala biliyan tara ($9bn) a duk shekara sakamakon wannan mummunar aiki da fataucin ma’adinai. Ya ce ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suna tauye wa gwamnati kudaden shiga, suna lalata muhalli, tare da haddasa rashin tsaro a yankunan da ake hakar ma’adinai.
Ya kara da cewa Special Mining Marshals sun taka muhimmiyar rawa wajen gano da kuma rushe wuraren hakar ma’adinai na haram, kama wadanda ke da hannu, da kuma tabbatar da tsaron ma’adinai tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Bunƙasa Ma’adinai da sauran hukumomin tsaro. A cewarsa, an rufe fiye da wurin hakar ma’adinai 500 a fadin kasar nan, tare da kama fiye da mutane 300 da ake zargi da wannan laifi. Duk da wadannan nasarorin, ya ce rashin isasshen kariya ta doka, karancin kudi, da rashin kayan zamani na lura da tsaro suna hana rundunar cimma cikakken nasara.
ACC Attah ya roki Majalisar Dokoki ta Kasa da ta karfafa tsarin doka da ke kula da bangaren hakar ma’adinai ta hanyar kafa karin dokoki masu tsauri kan masu laifi, da samar da isasshen tallafi ga hukumomin da ke da alhakin aiwatar da doka. Ya bayyana cewa ba tare da karfi daga doka da hadin kai tsakanin hukumomi ba, ba za a iya samun sakamako mai dorewa ba. “NSCDC na bukatar cikakken goyon bayan Majalisar Dokoki, gwamnatocin jihohi, da shugabannin al’umma domin samun nasara mai ma’ana. Dole ne mu dauki wannan yaki tamkar hakkin kowa ne, domin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba na lalata ci gaban kasa,” in ji shi.
Ya kammala da sake nanata kudurin NSCDC na kare albarkatun ma’adinai na Najeriya bisa umarnin Commandant General, Farfesa Audi. ACC Attah ya bukaci duk masu ruwa da tsaki – ciki har da sarakunan gargajiya, masu gadin yankuna, kungiyoyin fararen hula, da kungiyoyin masu hakar ma’adinai – da su hada kai da rundunar wajen musayar bayanai da kuma aikin hadin gwiwa. “Idan aka samu goyon bayan kowa, ingantattun dokoki, da hadin kai tsakanin hukumomi, Najeriya za ta iya farfado da bangaren ma’adinai nata, ta mayar da shi hanya ta bunkasar tattalin arziki mai dorewa,” in ji shi.





