Kwamandan Jihar Katsina na Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC), Commandant of Corps A.D. Moriki Acti Anim, a ranar Laraba 8 ga Oktoba, 2025, ya kai ziyarar ban girma ga Kwamandan Rundunar 213 Forward Operating Base na Sojojin Sama dake Katsina, wanda kuma shi ne Shugaban Rundunar Hadin Gwiwar Iskar Sama ta Ayyukan Hadarin Daji, Sashen II, Air Commodore G.I. Jibia, da kuma Kwamishinar Shari’a wato Babbar Lauya ta Jihar Katsina, Hajiya Fadila Mohammed Dikko. Ziyarar ta gudana ne a sansanin Sojojin Sama dake kan hanyar Daura da kuma Ofishin Ma’aikatar Shari’a dake kan hanyar Kano, duka a cikin garin Katsina.
A yayin ziyarar, Commandant Moriki ya jaddada kudirin Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa tare da kare muhimman gine-gine da kadarorin gwamnati a fadin kasar. Ya bayyana cewa wannan ziyara tana cikin shirin sada zumunta domin ƙarfafa haɗin kai, fahimtar juna da haɗin gwiwa mai ɗorewa tsakanin NSCDC, Sojojin Sama da Ma’aikatar Shari’a. Haka kuma, ya nuna godiya ga shugabannin biyu bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da bada goyon baya wajen cimma burin tsaro na bai daya.
A nasa jawabin, Air Commodore G.I. Jibia da Hajiya Fadila Mohammed Dikko sun taya Commandant Moriki murna bisa sabon nadin sa a Jihar Katsina, tare da yabawa hukumar NSCDC bisa kwazon ta da jajircewar ta wajen kare lafiya da tsaron al’umma. Sun kuma tabbatar da shirin su na ƙara ƙarfafa dangantaka mai kyau da inganta haɗin kai tsakanin hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar.
Daga cikin abubuwan da suka wakana a ziyarar har da musayar kyaututtuka, tattaunawar aiki kan batun tsaro da kuma ɗaukar hotunan haɗin kai da suka nuna girmamawa da amincewar juna tsakanin hukumomin.




