Kwamandan Jihar Ebonyi na Hukumar Tsaro da Kare Rayuka da Dukiyoyin Jama’a ta Najeriya (NSCDC), Kwamanda Francis Chika Nnadi, ya shiga cikin tawagar manyan jami’an hukumar da suka tarbi Babban Kwamandan Hukumar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, yayin ziyarar sa ta hukuma zuwa Jihar Anambra.
Kwamanda Nnadi na cikin tawagar da Mataimakin Babban Kwamanda Janar mai kula da Yankin Zone 13, Awka, Barista Nnamdi Nwannukwu, ya jagoranta tare da sauran kwamandojin jihohin yankin Kudu maso Gabas.
A cikin shirin ziyarar, Babban Kwamanda Janar zai gabatar da lacca a dakin taro na Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, mai taken “Amfani da Fasahar Artificial Intelligence Wajen Kare Muhimman Kadarorin Ƙasa da Gine-ginen Jama’a: Rawar da NSCDC ke Takawa.”
Taron na nuni da yadda hukumar ke ƙara dagewa wajen haɗa sabbin fasahohi cikin ayyukanta domin ƙarfafa tsaron ƙasa da bunƙasa ci gaba mai ɗorewa.
Bayan kammala laccar, Babban Kwamanda Janar zai ci gaba da rangadin sa zuwa Jihar Ebonyi a matsayin wani ɓangare na ziyarar aikin sa a duk faɗin yankin Kudu maso Gabas.



