Ijadola Ademolekun ya rubuto daga Ile-Ife, jihar Osun
An ruwaito cewa wata motar ’yan sanda, Toyota Buffalo Land Cruiser mai lambar rajista NPF 5594 D da chassis JTELU71JX0B027126, ta ɓace daga harabar Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya da ke Abuja.
Bacewar motar a cikin Louis Edet House, inda ake ɗauka a matsayin garkuwar tsaro, ya tayar da manyan tambayoyi kan yadda tsaro ke tafiya a cikin babbar cibiyar aiwatar da doka ta ƙasa.
Ga masu lura da al’amura, wannan ba ƙaramin abin kunya ba ne. Idan har motar gwamnati za ta iya ɓacewa daga cikin sansanin tsaron ’yan sanda, me hakan ke nufi ga lafiyar rayuka da dukiyoyin al’umma a sauran sassan ƙasar?
Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda na ɗaya daga cikin wuraren gwamnati da ake ganin ya fi kowane tsaro a Najeriya. An ce akwai jami’an tsaro a kowane ƙofa, ana gudanar da bincike sosai, kuma ana da na’urorin tsaro. Amma duk da haka, an ce motar ta ɓace ba tare da wata alama ba.
Lamarin ya jawo cece-kuce kan sahihancin tsarin tsaro a cikin rundunar ’yan sanda da ma sauran hukumomin gwamnati. Haka kuma ya ƙara hura wutar shakku kan yadda gwamnati ke iya kare dukiyarta, balle ta kare ta al’umma.
Tambayoyi masu tsauri sun taso. Ko sakaci ne ya haddasa hakan? Ko kuwa akwai hannu a ciki? A cikin tsarin da ba ya bin ka’ida, kuma inda alhakin kula bai da ƙarfi, duka biyun na iya yiwuwa – kuma duka biyun abin kunya ne.
Alamar da ke fitowa daga lamarin ba ta daɗi. ’Yan ta’adda da masu aikata laifuka a ƙasar sun riga sun samu ƙwarin guiwa daga raunin hukumomin tsaro. Wannan al’amari zai ƙara musu ƙarfin gwiwa. Idan har ’yan sanda ba za su iya tsare motocinsu ba, ta yaya za su iya tunkarar ’yan fashi a Zamfara, masu garkuwa da mutane a Kaduna, ko kuma barayi a Legas?
Rundunar ’yan sanda ba za ta iya yin shiru a kan wannan lamari ba. ’Yan Najeriya suna da haƙƙin samun amsa. Shin an sace motar ce, an sayar da ita, ko kuwa kawai ta “ɓace”? Wa ya yi sakaci? Kuma wane hukunci zai biyo baya? Yin shiru ko rufe gaskiya zai ƙara dagula dangantaka tsakanin ’yan sanda da al’umma, wanda tuni ke fama da matsalar amana.
Wannan rikici ya kamata a ɗauke shi a matsayin juyin juya hali. Rundunar ta kamata ta gyara kurakurai, ta tsaurara matakan tsaro, ta rungumi amfani da fasaha. Dole ne a iya bibiyar kowane kayan aiki, a san inda yake a kowane lokaci. Duk wani abu ƙasa da hakan ba za a lamunta da shi ba.
Amma wannan ba batun motar guda ɗaya ba ne kawai. Al’amari ne da ya shafi amincin tsarin tsaron Najeriya baki ɗaya. Raunin hukumomi, rashin ladabi, da halin rashin tsoro ga hukunci sun bar ’yan ƙasa cikin haɗari. Wannan Land Cruiser da ta ɓace, wata ƙwaƙƙwarar shaida ce ta tsarin da ya lalace.
Idan Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya tana son dawo da amincewar jama’a, dole ne ta yi aiki cikin gaggawa, gaskiya, da tsauri. ’Yan Najeriya na kallon abin da za a yi.
Domin kuwa, idan mota za ta iya ɓacewa a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda, gaskiya ne, babu wanda ya tsira.




