Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta tabbatar a hukumance da gano wani yunkurin juyin mulki da wasu manyan jami’an soji suka shirya.
Bayan kammala bincike mai zurfi, an tuhumi jami’an da aka samu da hannu a lamarin, kuma ana sa ran za su fuskanci shari’a a gaban kotun soja bisa ka’idoji da dokokin rundunar sojin Nijeriya.
DHQ ta jaddada kudurinta na tabbatar da da’a, biyayya, da kare tsarin mulkin dimokuradiyya, tare da tabbatar wa al’umma cewa za a bi doka da oda domin tabbatar da adalci da daukar matakin da ya dace.




