Hukumar Kwashe Gobara ta Ƙasa (FFS), Jihar Gombe, a ranar Juma’a ta karɓi tawaga daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Tarayya a wani ziyarar aiki domin gudanar da binciken gamsuwar jama’a da ingancin hidima na kwata na uku da na hudu (SERVICOM).
Mai karɓar baƙuncin tawagar shi ne Kwamandan Jiha, DCF Suleiman Mohammed Suleiman, a ofishinsa da ke Gidan Gwamnatin Tarayya, Gombe. Tawagar ta kasance ƙarƙashin jagorancin Mrs. Sarah Mandoni tare da rakiyar Mrs. Atta.
A lokacin nazarin, tawagar ta bayyana gamsuwarta da tsabtar muhalli, tsari, da kuma kwanciyar hankali da ake samu a ofishin Hukumar. Haka kuma, sun yaba da kyan kamanni, ƙwarewa, da ladabi na jami’an da suke bakin aiki.
Tawagar ta kuma jinjinawa Sashen Hulda da Jama’a saboda yadda yake sadarwa da jama’a cikin inganci, musamman ta hanyar shafinsu na Facebook da mutane da dama ke bi, wanda ya zama wata muhimmiyar kafa ta karɓar koke-koke, tambayoyi, da yabo daga jama’a.
A bisa ka’idojin SERVICOM, tawagar ta kuma yaba da yadda shugabancin Hukumar ke aiwatar da tsarin lada da hukunci domin ƙarfafa ma’aikatan da ke nuna bajinta, lamarin da ke inganta aiki, gaskiya, da ingantacciyar hidima ga al’umma.
A ƙarshe, tawagar ta yaba wa Kwamandan Jiha, DCF Suleiman Mohammed Suleiman, bisa ingantaccen jagoranci, tare da jinjinawa jajircewa da haɗin kan jami’ai da ma’aikatan Hukumar wajen inganta hidima da ƙara karfafa amincewar jama’a.


