Laftanar A.M. Yerima, jami’in Rundunar Sojan Ruwa na Najeriya da ya shiga takaddama da Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kwanan nan, ya tsira daga wani yunkurin bin diddigin da wasu ba a san ko su waye ba suka yi masa a daren Litinin a Abuja.
Majiyoyi sun bayyana cewa motocin Hilux guda biyu marasa lamba da ba su da wata alama ta hukuma sun fara binsa tun daga Filin Mai na NIPCO a kan titin Kubwa Expressway zuwa Gado Nasco Way. Yerima dai ya lura da motsin da ya zama abin zargi, inda ya dauki dabarun tsira domin kauce wa motoci masu bin sa.
Lamarin, wanda ya faru misalin karfe 6:30 na yamma, ya isa ga hukumomin tsaro, kuma an fara bincike a kai. Wata majiya da ta san lamarin ta ce ana takatsantsan wajen fitar da cikakkun bayanai saboda muhimmancin binciken.
Tun da farko, Yerima ya shiga takaddama da Ministan FCT, Nyesom Wike, kan wata muhawara da ta taso a wajen wani aikin rusau a Abuja — lamarin da ya haddasa mahawara da martani daga jama’a.
A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa Fadar Shugaban Kasa ta shiga tsakani, lamarin da ya sa hukumomin FCT suka janye kayan aikin rusau da aka tura zuwa filin da ake samun sabani a Gaduwa District.



