Taron 2025 People’s Security Monitor Security Summit and Recognition Award zai haɗa manyan shugabannin tsaro da masanan tsaro daga sassa daban-daban na ƙasar. Za a duba muhimman nasarorin tsaro da aka samu a matakin ƙasa tare da karrama jami’ai da masu sa kai da suka nuna bajinta da gaskiya a ayyukansu.
Manufar taron ita ce ƙarfafa nagarta, haɓaka ɗabi’ar aikin tsaro, da ƙara ƙaimin al’umma wajen goyon bayan hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Domin ƙarin bayani: pressgallery2013@gmail.com | 08055001816.



