Yayin da jama’ar Jihar Anambra ke shirin fita don kada ƙuri’unsu a zaɓen 2025, Babban Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC), Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, ya sake tabbatar da kudirin hukumar na kare rayuka da kuma tabbatar da tsaron muhimman kayan ginin ƙasa (Critical National Assets and Infrastructure – CNAI), tare da tabbatar da zaɓe mai inganci, lumana, da gaskiya.
Da yake jawabi ta bakin Mataimakin Babban Kwamandan da ke kula da harkokin Ayyuka, DCG Philip Ayuba, Farfesa Audi ya tabbatar wa jama’a cewa jami’an NSCDC da aka tura don aikin zaɓe sun samu cikakken horo da umarni na yin aiki da ƙwarewa, son kai, da girmama haƙƙin ɗan adam a duk lokacin zaɓen.
“Dalilin kasancewarmu a rumfunan zaɓe shi ne don kare jama’a, ba don tsoma baki ba. Muna nan ne domin tabbatar da yanayi mai aminci da kwanciyar hankali domin masu zaɓe su yi amfani da haƙƙinsu ba tare da tsoro ba,” in ji Farfesa Audi.
Ya kara da cewa, aikin hukumar ba kawai kare masu kada ƙuri’a ba ne, har da tabbatar da tsaron muhimman gine-gine da na’urori irin su wutar lantarki, samar da ruwa, hanyoyin sadarwa, da sauran kayayyakin more rayuwa da ke taimakawa wajen nasarar zaɓe da dorewar zaman lafiya a ƙasa.
“Mandatinmu ya wajabta mu kare abubuwan da ke tabbatar da ci gaban ƙasa, domin sahihancin kowanne zaɓe ya dogara ne ba kawai a kan tsaron masu kada ƙuri’a ba, har ma da tsaron tsarin da ke goya masa baya,” in ji shi.
Farfesa Audi ya jaddada cewa NSCDC za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa kundin tsarin mulki – na kare rayuka, gine-ginen gwamnati, da tabbatar da zaman lafiya yayin manyan ayyukan ƙasa. Ya gargadi jami’an hukumar da su kasance cikin shiri a kusa da ofisoshin INEC, gine-ginen gwamnati, da sauran muhimman wurare, yana mai jan kunnen cewa duk wani jami’i da ya aikata laifi ko nuna son kai na siyasa zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Babban Kwamandan ya kuma tabbatar da cewa NSCDC za ta ci gaba da aiki tare da Hukumar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, Rundunar Sojoji, da sauran hukumomin tsaro karkashin Kwamitin Hulɗa Tsakanin Hukumomin Tsaro kan Zaɓe (ICCES) domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana da gaskiya.
Ya roƙi jama’a, musamman masu kada ƙuri’a, da su kasance masu natsuwa, bin doka, da kuma haɗin kai da jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa tsaron rayukan al’umma, kare muhimman kadarorin ƙasa, da tabbatar da sahihancin zaɓe su ne manyan abubuwan da NSCDC ke baiwa muhimmanci.



