Jihar Anambra tana cikin natsuwa da zaman lafiya yayin da shirye-shirye ke ƙaruwa domin zaben gwamna da za a gudanar a ranar Asabar. ‘Yan sanda da aka tura don aikin zabe sun karɓi cikakken ikon tsaro a fadin jihar, suna tabbatar da yanayi mai aminci ga masu kada kuri’a da sauran al’umma.
Wannan zaman lafiya da tsari da ake gani a yanzu, sakamakon ziyarar aiki ta kwana biyu da Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP Olukayode Egbetokun, Ph.D., NPM, ya kai jihar, inda ya gudanar da tarurruka da muhimman masu ruwa da tsaki. Wadannan tattaunawa sun ƙarfafa haɗin kai da gina amincewar jama’a kafin zaben.
A halin yanzu, Barista Taiwo Lakanu, fdc, tsohon Mataimakin Babban Sufeton ‘Yan Sanda (DIG) kuma Shugaban Kwamitin Tsayayye na PSC kan Harkokin ‘Yan Sanda, yana jagorantar tawaga mai ƙarfi ta jami’an PSC zuwa Jihar Anambra. Manufarsu ita ce su sa ido kan ayyukan ‘yan sanda, su tabbatar da ƙwarewa da ƙwazo, tare da karfafa musu gwiwa wajen gudanar da aiki yadda ya kamata a lokacin zabe.
A cikin aiwatar da kundin aikinta na kare dimokuraɗiyya da tabbatar da zabe mai sahihanci da lumana, Hukumar ta kuma fitar da lambobin waya na musamman domin ‘yan ƙasa su rika bayar da rahoton yadda ‘yan sanda ke gudanar da aikinsu yayin zabe. Ana ƙarfafa jama’a da su yi amfani da waɗannan lambobi domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Lambobin Waya na PSC Domin Jihar Anambra:
Anambra Central:
- 08064696711
- 08035909482
- 08039398301
Anambra South:
- 08034741057
- 08033497350
- 08033830073
Anambra North:
- 08033145592
- 08037505436
- 08037416438
Dakin Kula da Harkokin Zabe (Situation Room):
- 08033145592
- 08055480701
- 08033345362
- 08185241907
- 08064696711
DIG Lakanu ya jaddada kudirin Hukumar na ci gaba da goyon baya ga Hukumar ‘Yan Sanda ta Ƙasa domin tabbatar da cewa zabubbuka suna gudana cikin ‘yanci, gaskiya, da sahihanci. Ya ce PSC za ta ci gaba da kare masu kada kuri’a da kayan zabe tare da tabbatar da yanayi mai kyau da natsuwa a wuraren zabe.
Kwamishinan ‘Yan Sanda da aka tura domin kula da zabubbuka, CP Abayomi Shogunle, Ph.D., fsi, ya iso jihar tun tuni, kuma ya tsara ingantaccen shirin tsaro domin tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana, gaskiya, da amana.
Haka kuma, DIG Ben Okolo, DIG mai kula da Sashen Leken Asiri na ‘Yan Sanda, ana sa ran shi ne zai jagoranci rundunar ‘yan sanda a lokacin zaben.



