Hukumar People’s Security Monitor (PSM) tana farin cikin sanar da kira ga jama’a da su gabatar da sunayen mutanen da za a karrama kafin gudanar da Taron Tsaro da Lambar Girmamawa na Shekara ta 2025, wanda za a yi a ranar Laraba, 10 ga Disamba, 2025, a Nigerian National Merit Award House, Maitama, Abuja.
Wannan babban taron kasa zai zama dandali na tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin masana harkar tsaro, masu tsara manufofi, da sauran masu ruwa da tsaki wajen duba halin da tsaro ke ciki a Najeriya. Haka kuma, taron zai karrama mutane da cibiyoyi nagari da suka nuna gaskiya, ƙwarewa, da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da dorewar kasa.
Lambar Girmamawa ta People’s Security Monitor ta shafi dukkan bangarorin tsaron Najeriya, ciki har da Sojoji, ‘Yan Sanda, Civil Defence, Hukumar Shige da Fice (Immigration), Hukumar Kwastam, Hukumar Kula da Gobara, NDLEA, DSS, da sauran hukumomin tsaro, inda za a karrama jami’ai – wadanda ke aiki da wadanda suka yi ritaya.
Bugu da ƙari, an bude damar karramawa ga ‘yan kasa masu gaskiya daga jama’a, ciki har da shuwagabannin al’umma, ‘yan jarida, malamai, da ‘yan kasuwa, wadanda suka taka rawar gani wajen gina zaman lafiya, haɗin kai, da tsaron kasa.
Ka’idojin Neman Girmamawa:
Duk wanda ke son gabatar da sunan wani ya hada da:
- Takaitaccen tarihin rayuwa (CV) na wanda ake ba da shawara a kansa.
- Takalman shaida ko hujjojin nasarori (idan suna akwai).
- Adireshi, lambar waya, da adireshin imel na wanda ake ba da shawara a kansa.
- Sunan, cibiyar aiki, adireshi, da sa hannun wanda ya ba da shawarar.
- Takaitaccen bayani (ba fiye da kalmomi 200 ba) da ke bayyana irin gudunmawar da wanda ake shawara ya bayar wajen tsaro ko walwalar jama’a.
Ranar Rufe Karɓar Sunaye:
Dole a karɓi dukkan sunaye kafin Juma’a, 22 ga Nuwamba, 2025.
Tura Bayanai da Tambayoyi:
A tura dukkan bayanai da tambayoyi zuwa:
Shugaban Kwamitin Shirya Taro
Isiaka Mustapha
Lambar waya: 08055001816
Imel: pressgallery2013@gmail.com
Ku kasance tare da mu wajen girmama jarumai, masu kishin kasa, da kwararrun da ke hidima ga ci gaban Najeriya.
Tsaron Najeriya Nauyinmu Ne Gaba ɗaya… Mu Girmama Jarumai Na Gaskiya!
Sa hannu:
Hukumar Gudanarwa, People’s Security Monitor (PSM)
Ranar: 26 ga Oktoba, 2025



