Hukumar People’s Security Monitor (PSM) ta bayyana cewa za ta gudanar da Taron Tsaro da Lambar Girmamawa na 2025 a ranar Laraba, 10 ga Disamba, 2025, a Nigerian National Merit Award House, Maitama, Abuja.
Wannan taron mai muhimmanci zai zama dandali na tattaunawa da nazari kan halin da tsaro yake ciki a Najeriya, inda masana tsaro, masu tsara manufofi, da sauran masu ruwa da tsaki za su tattauna hanyoyin da za su kara tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasa.
Baya ga tattaunawar dabaru, za a kuma karrama ‘yan Najeriya masu jajircewa da gaskiya da kuma ƙwarewa a fannin tsaro, wadanda suka bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa.
Sabon tsarin taron na bana zai kasance abin tarihi, inda za a sami jawaban manyan baki, muhawarar kwamitoci, da bada lambobin yabo ga mutanen da suka yi fice a harkar tsaro.
Don karin bayani ko halarta, a tuntubi Sakateriyar taron ta:
📞 +234 (0) 8055001816
📧 info@pressgallery2013@gmail.com



