KOMANDAN BALA BAWA BODINGA YA KADARDA SABON OFISHIN NSCDC A NA’IBAWA EASTERN BYPASS, KANO

Kwamandan Jihar Kano na Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC), Kwamanda Bala Bawa Bodinga, ya kaddamar da sabon ofishin hukumar a Na’ibawa Eastern Bypass dake cikin karamar hukumar Kumbotso, Jihar Kano.

Yayin kaddamar da ofishin, Kwamanda Bodinga ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma wajen tabbatar da tsaro, yana mai cewa batun tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, ba wai jami’an tsaro kadai ba. Ya bukaci al’umma da shugabanninsu da su ci gaba da baiwa hukumar hadin kai don ganin an samu zaman lafiya mai dorewa.

Kwamandan ya kuma gode wa shugabannin al’ummar Na’ibawa karkashin jagorancin Arc. Abubakar Ibrahim Diso bisa gina wannan gini, tare da kiransu da su ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumar domin ingantaccen aiki da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Haka kuma, Kwamanda Bodinga ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa an kafa tawagar Rapid Response Team domin gudanar da sintiri a kowane lokaci, don tallafa wa jami’an da ke ofishin wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ya gargadi jami’ansa da su guji aikata rashawa ko take hakkin ‘yan kasa, yana mai jan hankalinsu da su kasance masu bin ka’idoji da ladabtarwa wajen gudanar da ayyukansu bisa manufofin hukumar.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar al’ummar Na’ibawa Eastern Bypass, Arc. Abubakar Ibrahim Diso, ya tabbatar wa Kwamanda Bodinga da cikakken goyon bayan al’umma ga hukumar, tare da bayyana cewa suna da shirin inganta walwalar jami’ai da kyautata ayyukan yau da kullum a ofishin. Ya ce suna da shirin gina karin gini wanda zai kunshi aƙalla dakuna goma sha biyar (15) domin tallafa wa ayyukan hukumar a yankin.

Arc. Diso ya bayyana cewa kafin zuwan ofishin NSCDC yankin na fama da matsalolin ‘yan daba, satar wayoyi, da sauran laifuffuka, amma tun bayan kafa ofishin, tsaro ya inganta sosai har farashin filaye ya fara tashi a yankin.

A karshen taron, Kwamanda Bodinga cikin karamcinsa ya ba da gudunmawar takardu rims biyu (2) na A4 da wasu kayan aiki domin tallafawa sabon ofishin hukumar da aka kaddamar.

  • Keji Mustapha

    Related Posts

    Ooni of Ife Visits Nigeria Immigration Service Headquarters for Diplomatic Passport Renewal

    His Imperial Majesty, the Ooni of Ife, Oba Adeyeye Enitan Babatunde Ogunwusi, Ojaja II, on Tuesday visited the Headquarters of the Nigeria Immigration Service (NIS) in Abuja for the renewal…

    Osun NSCDC Decorates 267 Newly Promoted Officers

    The State Commandant of the Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), Osun State Command, Commandant Igbalawole Sotiyo, has decorated two hundred and sixty-seven (267) officers recently promoted in the…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ooni of Ife Visits Nigeria Immigration Service Headquarters for Diplomatic Passport Renewal

    Ooni of Ife Visits Nigeria Immigration Service Headquarters for Diplomatic Passport Renewal

    Osun NSCDC Decorates 267 Newly Promoted Officers

    Osun NSCDC Decorates 267 Newly Promoted Officers

    Osun NSCDC Decorates 267 Newly Promoted Officers

    Osun NSCDC Decorates 267 Newly Promoted Officers

    “Without Security, Development Cannot Thrive” — Oyo Deputy Governor as NSCDC Decorates 160 Promoted Officers

    “Without Security, Development Cannot Thrive” — Oyo Deputy Governor as NSCDC Decorates 160 Promoted Officers

    Federal Fire Service Launches Nationwide Performance Management Reform Initiative

    Federal Fire Service Launches Nationwide Performance Management Reform Initiative

    Oluwo Decorates NSCDC Aide, Akintunde Wale, on Promotion to Deputy Superintendent of Corps

    Oluwo Decorates NSCDC Aide, Akintunde Wale, on Promotion to Deputy Superintendent of Corps