A ci gaba da ƙoƙarinsa na ƙarfafa haɗin gwiwa domin bunƙasa da faɗaɗa ayyuka a National Fire Academy na Federal Fire Service, Controller General of Fire (CGF), Dr. Olumode Samuel Adeyemi, FCNA, ACTI, tare da wasu manyan jami’an hukumar, sun kai ziyara ta girmamawa ga Mai Martaba Luka Ayedoo Nizassan III, Etsu na Kwali kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya, a fadarsa da ke Kwali, Abuja.
CGF Adeyemi ya nuna godiyarsa ga Mai Martaba bisa kyakkyawar alaƙa da haɗin kai da yake ba wa hukumar, musamman wajen tallafawa National Fire Academy da ke cikin yankin masarautarsa. Haka kuma ya yaba wa sarki da al’ummarsa bisa goyon baya da kulawar tsaro da suke bai wa makarantar.
A martaninsa, Mai Martaba Etsu Kwali, Luka Ayedoo Nizassan III, ya taya CGF Adeyemi murna bisa irin jagorancin da yake bayarwa, tare da tabbatar masa da cigaban haɗin gwiwa, ƙarfafa zumunci da ci gaba da goyon baya, domin tabbatar da cewa National Fire Academy ta zama cibiyar koyi a fannin horar da jami’an kashe gobara a fadin ƙasar nan.





