Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Oyo ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruq bisa zargin kona tsohuwar masoyiyarsa, Omolola Hassan, bayan wata sabani da ta barke tsakaninsu a cikin barikin sojoji da ke Ibadan, babban birnin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya zuba mata fetur sannan ya kunna wuta a jikinta lokacin da aka samu rikici tsakaninsu sakamakon rushewar dangantakar soyayyarsu. Shaidu sun ce jami’an soji da ke cikin barikin sun yi gaggawar kai agaji, suka kashe wutar sannan suka garzaya da wadda abin ya shafa zuwa asibitin Yawiri Hospital, Akobo, domin kula da lafiyarta.
Wani masanin tsaro, Zagazola Makama, wanda ya wallafa cikakkun bayanai kan lamarin a shafinsa na X (wanda a da ake kira Twitter), ya bayyana cewa wanda ake zargin ya ce shi da wadda abin ya shafa sun dauki rantsuwa cewa ba za su taba rabuwa ba. Sai dai, lokacin da soyayyar ta mutu, wanda ake zargin ya fusata ya kuma aikata wannan mummunan aiki.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa bincike na ci gaba da gudana a kan shari’ar.
Wannan lamari na cikin jerin tashin hankali da ke yawaita a sassan Najeriya sakamakon rushewar dangantakar soyayya. A watannin baya-bayan nan, an ruwaito wasu makamantan lokuta inda ma’aurata ko masoya suka kai wa juna hari ta hanyar kona ko aikata wasu munanan ayyuka.
Hukumomi sun ci gaba da kira ga jama’a da su nemi hanyar lumana wajen warware sabani tare da kai rahoton duk wata barazana ko alamar tashin hankali a cikin gida kafin ta kai ga mummunan sakamako.





