Sabon kwamandan hukumar tsaro ta Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) na jihar Jigawa, Commandant Muhammad Kabiru Ingawa, ya tabbatar da kudirinsa na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin ƙarfafa zaman lafiya, adalci da amincewar jama’a ga gwamnati.
Commandant Ingawa ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin kwamishinan hukumar Public Complaints Commission (PCC), Mai Girma Hon. Barde Usman Shehu Hadejia, wanda ya kai masa ziyarar ladabi a hedkwatar hukumar NSCDC dake Dutse.
A cikin jawabinsa, kwamandan ya tarbi kwamishinan da tawagarsa cikin farin ciki tare da nuna godiya bisa wannan ziyara. Ya tabbatar da cewa hukumar NSCDC za ta ci gaba da yin aiki tare da PCC domin magance koke-koke na jama’a, kare ‘yancin bil’adama da kuma tabbatar da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.
Ya kara da cewa, a karkashin jagorancinsa, NSCDC za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya, adalci, gaskatacciyar aiki da kuma kwarewa wajen aiwatar da nauyin da doka ta dora mata.
A nasa bangaren, Hon. Barde Usman Shehu Hadejia ya taya Commandant Ingawa murna bisa nadinsa a matsayin sabon kwamandan jihar Jigawa, tare da yabawa hukumar NSCDC bisa jajircewarta wajen kare muhimman kadarorin kasa, tsaron al’umma, da kuma goyon bayan hukumomin farar hula. Ya kuma bayyana shirinsu na ƙarfafa haɗin kai da NSCDC musamman wajen wayar da kai ga jama’a, sasanta rikice-rikice da kuma kare ‘yancin ɗan adam.
Dukkan shugabannin sun jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin hukumomi domin cimma zaman lafiya mai dorewa, tsaro da ingantaccen gudanar da ayyuka. Sun kuma bayyana aniyarsu ta ci gaba da ƙarfafa wannan haɗin kai domin amfanin jama’ar jihar Jigawa da Najeriya baki ɗaya.
Ziyarar ta haɗa da saƙonnin fatan alheri, tattaunawa kan shirin haɗin gwiwa a nan gaba, da kuma tabbatar da burin haɗin kai domin inganta zaman lafiya, adalci, da tsaron jama’a a fadin jihar.





