A yayin bikin ƙaddamar da Kwamitin Naɗa-naɗe na Majalisar Wakilai kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba, Mataimakin Kwamanda na Rundunar Musamman ta NSCDC kan Ma’adinai, ACC Onoja John Attah, ya jaddada bukatar ƙarfafa tsarin doka da sanya hukunci mai tsanani ga masu aikata wannan laifi. Ya bayyana cewa, hakan yana da matuƙar muhimmanci wajen dakile barna da asarar tattalin arziki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ke haifarwa a ƙasar.
ACC Onoja ya bayyana cewa Najeriya na asarar kuɗi kimanin dalar Amurka biliyan tara a kowace shekara sakamakon harkar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wanda ke rage wa gwamnati damar samun kuɗaɗen shiga don ayyukan raya ƙasa. Ya ce tun bayan kafa rundunar Mining Marshals ta NSCDC a watan Maris, shekara ta 2024, an kama mutane sama da dari biyar da ake zargi da irin wannan laifi, kuma kimanin dari biyu da saba’in daga cikinsu suna fuskantar shari’a a kotuna daban-daban. Ya ce sai an kafa dokoki masu tsauri da hukunci mai tsanani kafin a iya samun cikakken nasara a wannan yaƙi.
Ya bayyana wasu ƙalubale da suka hana nasarar wannan yaki, ciki har da raunin tsarin doka, rashin hukunci mai tsanani, jinkirin shari’a, da kuma rawar da kungiyoyin laifi da wasu manyan mutane ke takawa wajen kare masu laifi. Onoja ya roƙi Majalisar Wakilai da ta samar da sabbin dokoki da za su tanadi tara mai tsanani, daurin lokaci mai tsawo, da kuma gaggawar yanke hukunci ga masu laifi domin tsoratar da sauran masu shirin aikata irin wannan laifi.
Ya kuma ce mafi yawan wuraren da ake hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suna cikin dazuzzuka, duwatsu da yankunan da suka da wuya a isa. Wannan, a cewarsa, yana kara wahalar da aikin sa ido da farmaki. Don magance wannan, NSCDC ta fara amfani da jiragen ɗan Adam marasa matuki (drones), fasahar taswira ta tauraron dan adam, da sauran na’urorin zamani domin gano wuraren kafin a kai farmaki.
ACC Onoja ya kara da cewa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati yana da matuƙar muhimmanci. Ya kawo misali da haɗin gwiwar da ke tsakanin NSCDC da Hukumar Bincike da Cigaban Kayan Halitta (RMRDC), wadda take taimaka musu da bayanan kasa, ƙwararrun masana, da kuma binciken shaidar laifi domin tabbatar da nasarar shari’u.
A ƙarshe, ACC Onoja ya roƙi kwamitin Majalisar Wakilai da ya sanya muhimmanci ga gyaran dokokin da suka shafi hakar ma’adinai. Ya ce, “Sai mun bai wa hukumomin tsaro ƙarfafa ta hanyar doka kafin su iya murƙushe masu laifi da gaske.” Ya tabbatar da cewa NSCDC za ta ci gaba da wannan yaƙi da ƙwazo, ƙwarewa da tsayin daka domin kare arzikin ƙasa, muhalli, da tabbatar da cewa halattattun masu hakar ma’adinai suna cin gajiyar albarkatun ƙasa cikin gaskiya.




