Kwamandan Jiha na Hukumar Tsaro ta Ƙasa da Kare Fararen Hula (NSCDC) reshen Jihar Kano, Commandant Bala Bawa Bodinga, a ranar Alhamis, ya karɓi bakuncin Babbar Darakta ta Hukumar Tsarin Birane da Ci Gaban Kano (KNUPDA), Arc. Hauwa Hassan T/Wada, a ofishinsa.
Ziyarar ta bayar da dama ga hukumomin biyu su tattauna hanyoyin haɗin gwiwa don inganta tsarin birane da kuma ƙarfafa tsaro a cikin jihar.
A ƙarshen ganawar, shugabannin biyu sun amince da yin aiki tare domin cimma haɗin kai mai amfani wa juna, wanda zai taimaka wajen samar da ci gaban ɗorewa da tabbatar da tsaro da kyakkyawan tsari na birane ga al’ummar Jihar Kano.
Commandant Bodinga ya tabbatar da kudirin NSCDC na ci gaba da tallafawa ƙoƙarin KNUPDA wajen kare muhimman gine-ginen gwamnati da tabbatar da bin ka’idojin da gwamnati ta shimfiɗa a fannin ci gaban birane. Ya jaddada cewa tsari mai kyau da tsaro suna tafiya hannu da hannu wajen gina al’umma mai zaman lafiya da cigaba.
A nata jawabin, Arc. Hauwa Hassan ta yabawa jagorancin Commandant Bodinga bisa nuna kwazo da jajircewa wajen gudanar da aikinsa. Ta kuma bayyana farin ciki da fatan alheri cewa wannan haɗin gwiwar zai haifar da sakamako mai kyau, musamman wajen magance matsalolin gine-gine ba bisa ka’ida ba, mamaye filaye, da sauran matsalolin tsaro da suka shafi tsarin birane a jihar.




