Hoto: Farfesa Ahmed Abubakar Audi, Babban Kwamandan NSCDC
Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Jama’a da Kare Muhalli (NSCDC), Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya bayyana cewa, akalla mutane 500 da ke gudanar da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba an kama su, yayin da 270 daga cikinsu ke fuskantar shari’a a jihohi daban-daban na ƙasar.
Farfesa Audi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin ƙaddamar da kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai kan fasa kwaurin ma’adinai. A madadinsa, Mataimakin Kwamandan Corps John Attah ne ya wakilta shi. Ya jaddada kudirin hukumar na ci gaba da aiki kafada da kafada da Majalisar Dokoki da sauran hukumomin da abin ya shafa domin kawo ƙarshen fasa kwaurin ma’adinai da kare dukiyar ƙasa.
Ya bayyana cewa, NSCDC ta kafa rundunar musamman mai suna Mining Marshals Task Force domin yaƙar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da kuma hana asarar kuɗaɗen shiga ga gwamnati. Ya ce kafa wannan runduna wani mataki ne na gaggawa da nufin ƙarfafa aiwatar da doka, tabbatar da gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da cewa harkar hakar ma’adinai tana gudana bisa ƙa’idojin gwamnati da muradun ƙasa.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin wucin gadi, Hon. Sanni Abdulraheem, ya jaddada cewa kwamitin na da cikakken niyya na toshe hanyoyin asarar kuɗaɗen gwamnati tare da tabbatar da gaskiya a fannin ma’adinai. Ya bayyana hakar ma’adinai ba bisa doka ba a matsayin “annoba mai illa ga tattalin arziki da muhalli,” inda ya yi alkawarin cewa za su tabbatar da cewa duk kuɗaɗen da ake samu daga albarkatun ƙasa na Najeriya suna amfani ne don bunƙasar tattalin arzikin ƙasa. Abdulraheem ya kuma tabbatar da cewa kwamitin zai ƙara ƙarfafa sa ido, inganta hanyoyin bibiyar kuɗaɗen shiga, tare da tallafawa hukumomin tsaro kamar NSCDC wajen kawar da masu fasa kwaurin ma’adinai a faɗin ƙasa.




