Hoto: CG Olumode Adeyemi Samuel
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta kaddamar da Makon Tsaron Gobara na 2025, wanda ya kunshi yunkurin wayar da kan jama’a a makarantu, duba kasuwanni, gwaje-gwajen kare gobara a al’umma, tantance hadurran masana’antu da kuma nuna dabarun kare gobara a bainar jama’a a dukkan jihohin kasar da Abuja.
Yayin da yake bude makon a Hedikwatar Hukumar a Abuja, Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Samuel Olumode Adeyemi, ya ce an kirkiro wannan shiri ne domin rushe halin sakaci da rashin daukar martanin gaggawa kan batun gobara da aka saba gani a kasar — halin da aka fi fassara ta cikin maganar nan, “ba ni bane zai shafa.”
Adeyemi ya bayyana cewa jigon wannan shekara, “Gina Al’adar Tsaron Gobara a Fadin Nijeriya: Warware Tunani na ‘Ba Ni Bane Zai Shafa’”, na magana ne kai tsaye kan dabi’un da tsawon shekaru suke hana nasarar matakan kare gobara a gidaje, kasuwanni, ofisoshi da wuraren jama’a. Ya gargadi cewa gobara “ba ta bambanta mutane,” sannan sakacin mutane kan jawo asarar da ba za a iya gyarawa ba.
Shugaban ya ce Hukumar tana aiwatar da sauye-sauyen zamani a ayyukanta bisa ga Manufar Sabon Fata ta Shugaba Bola Tinubu, tare da goyon bayan Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji Ojo. A cewarsa, matakin sauyi na gaba zai mayar da hankali kan tsarin gano gobara ta hanyar fasaha, hanzarta isar da agaji, inganta jin dadin ma’aikata da kara hada kai da al’umma. Ya kara da cewa wadannan matakai ne za su taimaka wajen cimma matakin tsaron gobara da ake bukata domin tallafawa tushen tattalin arzikin Naira tiriliyan daya da shugaban kasa ya kudurta.
A lokacin bikin, Adeyemi ya mika Takardun Banki ga iyalan jami’an kashe gobara da suka rasu ko suka ji rauni a bakin aiki, a karkashin Tsarin Inshorar Rayuwa, inda ya ce hakan tunatarwa ce ga irin sadaukarwar da jaruman hukumar ke yi. Ya yaba wa kamfanonin inshora, abokan hulda da Sashen Harkokin Musamman saboda rawar da suka taka, tare da shawartar wadanda suka amfana da su kula da kudin yadda ya kamata.
An kuma gabatar da medaloli da kofunan gasar “CG’s Cup”, wadda Alhaji Kabir Lateef ya dauki nauyi. An bayyana gasar a matsayin wadda za ta kasance kowace shekara, domin karfafa hadin kai, ladabi, jajircewa da zumunci a tsakanin jami’an Hukumar Kashe Gobara, tare da shirin fadada ta zuwa wasu hukumomi nan gaba.
Yayin da yake karin bayani kan taken makon, Adeyemi ya jaddada cewa tsaron gobara nauyi ne na kowa da kowa, ba mutum daya kadai ba. Ya shawarci ‘yan Najeriya su fara aiwatar da matakan tsaro a rayuwarsu ta yau da kullum — kamar saka na’urar gano hayaki, tabbatar da hanyoyin tsira suna budadde, duba kwandunan gas, kashe kayan lantarki idan ba a amfani da su, da bin ka’idojin gine-gine.
Haka kuma, ya bukaci gwamnatoci a matakai daban-daban su daina tunanin “Ba Ni Bane Zai Shafa” ta hanyar zuba jari a famfunan kashe gobara, hada tsaron gobara da tsarin tsaron kasa, tare da farfado da martabar hukumomin kashe gobara a fadin kasar.
Adeyemi ya nuna godiya ga abokan hulda da masu ruwa da tsaki wadanda hadin kansu ke kara inganta aikin hukumar na kare rayuka, dukiya da muhalli. Ya yaba da jajircewar jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, tare da kira ga ‘yan Najeriya su rungumi sabuwar dabi’a ta tsaro, kula da kai da kishin kasa.
Ya ce, “Mu maye gurbin tunanin ‘Ba Ni Bane Zai Shafa’ da ‘Ni ne ke da alhakin tsarona da tsaron wasu,’” in ji shi.



